Sakataren hukumar kula da jin dadin mahajjata na jihar Nasarawa SPWB Abubakar Nalarabe ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta sake duba maganan kudin kujeran aikin hajin bana domin rage wa.
Abubakar ya fadi haka ne ranar Lahadi a wajen taron wayar da kai da aka shirya wa Maniyyata aikin hajin bana daga jihar.
Abubakar ya yi kira ga wadanda har yanzu ba su kammala biyan kudaden kujerunsu ba da su gaggauta yin hakan cewa hukumar ta kara musu mako guda.
Bayan haka kuma ya shawarci Maniyyatan da su tabbata sun sami cikakken bayanai daga hukumar kafin su biya kudaden tafiyar su domin gujewa baragurbin ma’aikata da zasu iya zambatarsu.
Da yake tofa albarkacin bakinsa a wajen taron sarkin Doma Aliyu Ogah-Onawo ya gargadi maniyyatan da su bi dokokin kasar Saudiyya a lokacin aikin Haji.