Hasarar Dukiya: Mutanen karamar hukumar Babura na bukatar Taimako

0

Jami’I mai kuka da harkar yada labaran na karamar hukumar Babura Sulaiman Doro ya ce a ranar 27 ga watan Yuni iska mai karfi ta yi sanadiyyar rushewar gidaje sama da 220, runfuna, makarantu da cibiyoyin kiwon lafiya a kauyukan Jigawar Dan-Alli, Gurfai, Manga, Unguwar Tsamiya da Yarkirya, jihar Jigawa.

Ya fadi haka ne da yake hira da kamafanin dillancin labaran Najeriya a garin Dutse.

Suleiman Doro ya ce mutanen da wannan ibtil’I ya auka akan dukiyoyinsu na rokon gwamnati da ta gaggauta kawo musu dauki.

Wanda ya yi magana a madadin mutanen kuma ma’aikacin asibiti a jihar Dan-Ali Usman Madawaki, ya ce a yanzu haka mutanen sun koma zama da makwabtansu domin basu da wurin zama tun bayan rasa gidajen nasu.

Kansila mai kula da da ci gaban alu’mma na karamar hukumar Babura Ahmed Mohammed ya ce zai ba da gudunmawar kayayyakin agaji ga mutanen kauyukan da abin ya faru.

Ya kuma yi kira ga hukumar kula da bada agaji na jihar SEMA, kungiyoyi masu zaman kansu da attajiran jihar da su aiko da ko wani irin taimako ne zuwa wadannan kauyuka.

Share.

game da Author