Harkalla: EFCC ta sha alwashin iza keyar tsohon ministan shari’a zuwa kotun Amurka

0

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta na yin dukkan wasu shirye-shiryen da suka wajaba, domin iza keyar tsohon ministan kasar nan, Mohammed Adoke, zuwa Amurka domin ya amsa caje-cajen tuhumar da ake yi masa.

Lauyan EFCC, Johnson Ojogbane shi ya bayyana haka a yau Talata, a Abuja. Hukumar dai ta gurfanar da Adoke da kuma wasu kafanonin hakar danyen mai, Shell da Eni a bisa zargin da ake yi musu na yin harkallar dalar Amurka har bilyan 1.3.

An ce wadannan kamfanonin hakar mai dai sun biya kudin ne a cikin asusun ajiyar gwamnatin tarayya a London, domin mallakar rijiyar mai, mai lamba OPL 245, wadda ake ikirarin ta fi kowace rijiyar mai albarka a fadin Afrika.

Daga nan ne sai Adoke, a lokacin ya na ministan shari’a ya bada umarnin a karkatar da kudin zuwa asusun ajiya na banki, mallakar ministan man fetur na lokacin, Dan Etete. Inda nan take aka yi wata asarkala aka karkatar da dala milyan 800.

An dai yi ittifakin cewa akasarin wadannan kudade su na aljihun manyan jami’an gwamnatin tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan, ciki har da shi Adoke din, wanda har yanzu ya kekasa kasa ya ce bai ci nanin ba.

A ranar karshe ta baya-bayan nan alkali Mai Shari’a John Tsoho, ya tsaida ranar 13 Ga Yuni ranar da za a gurfanar da Adoke da sauran dukkan wadanda ake zargin ciki har da Etete.

Sai dai kuma a yau Talata din ne lauyan EFCC, Ojogbane ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai cewa ba za a iya ci gaba da shari’ar ba, saboda jami’an hukumar sun kasa cafko Adoke da sauran wadanda ake zargi din.

Idan ba amanta ba, Adoke ya taba shan alwashin fitowa daga buyar da yak e yi, zai mika kan sa ga EFCC, amma daga baya sai ya canja shawara, a bisa zargin cewa hukumar ba za ta yi masa adalci ba. Har yanzu dai ya yi layar zana.

Wadanda ake zargin dai su ne: Mohammed Adoke, Aliyu Abubakar, ENI Spa, Ralph Wetzels, Casula Roberto, Pujatti Stefeno, Burrafati Sebestino da kuma kamfanin Malabu Oil and Gas tare da wasu kamfanonin kasashen waje guda biyu.

Share.

game da Author