Hukumar kula da ingancin abinci ta kasar Saudi Arabia ta lalata daruruwan gororin ruwan ZamZam na jabu da ta gano wasu kamfanoni suna yi.
Jami’an hukumar sun kai ma wadannan gidajen da ake sarrafa ruwar ZamZam din na jabu ne farmaki bayan sun gano hakan.
Jaridar kasar Saudi mai suna Saudi Gazette ne ta rubuta wannan labari in da ta ce mahukuntar kasar sun gano cewa mutane na sarrafa ruwan ZamZam na jabu sannan suna siyar wa mutane saboda tsananin bukata da mutane sukeyi mata musamman yanzu da ake neminsa domin yin buda baki a watan Ramadan.
Hukumar ta gargaɗi mutane su yi kaffa-kaffa da irin ruwan da zasu siya domin yin amfani dashi.
Hukumar ta sanar da amincewa da wasu shaguna da zasu dinga siyar da ruwan.
A garin Madina ma an kama wasu masu sai da ruwan famfo a matsayin ruwan Zamzam inda hukumomi suka kwace sama da kwalabe 3000 na ruwar da ba na ZamZam bane.
Hukumomin kasar sun ce ba za suyi kasasa ba wajen hukunta duk wanda aka samu yana yin irin wannan Algushshu a kasar.