Gwamnatin Najeriya ta ce idan ta sami nasarar kammala shirye-shiryen da take yi na fara fitar da doya zuwa kasashen waje, Kasar za ta iya samun kudaden shiga da ya kai biliyan takwas a kowace shekara.
Ministan aiyukkan gona Audu Ogbeh ya sanar da hakan yayin da kwamitin da ke kokakarin kirkiro da dabarun fitar da doya zuwa kasashen waje suka ziyarce shi a Abuja.
Ya ce shirin fitar da doya zuwa kasashen waje wanda zai fara daga ranar 29 ga watan Yuli zai samar wa kasa da kudaden shiga.
Ogbeh ya bayana cewa kasar Ghana na samun biliyoyin kudi wajen kasuwancin doya da take da kasashen duniya.
’’ Idan kasar Ghana na samun kudade kamar haka Najerya za ta iya samun ninki hudu na abinda da Ghana ta ke samu’’.
‘’Ina so wannan kwamitin ta binciko dabarun da sawwaka wa manoman doya musamman traktocin huda.
Shugaban kwamitin Simon Irtwange y ace kwamitin na aiki da International Institute of Tropical Agriculture, IITA domin horar da manoma da kuma samar da ingantattun irin doya.