Gwamnatin jihar Zamfara za ta dauki ma’aikatan ungozoma 56 domin shawo kan matsalar karancin ma’aikatan kiwon lafiyar jihar.
Sakataren hukumar kula da aiyukkan asibitoci na jihar Zamfara Muhammad Adamu ne ya sanar da haka a taron da wata kungiya mai zaman kanta mai suna ‘Maternal, Newborn and Child Health’ (MNCH2) Project’ ta shirya a garin Gusau ranar Talata.
Adamu ya ce hakan da gwamnatin jihar Zamfara ta yi zai samar da nagartacciyar kiwon lafiya a kauyukan jihar.
‘’Mun fara daukan ungozoma wanda bayan mun kammala horas da su zamu tura su aiki a manyan asibitocin jihar da kuma asibitocin dake karkara’’.
Wani jami’in kungiyar ‘Save The Children International’ Isah Ibrahim ya ce hakan da gwamnatin jihar Zamfara ta yi zai inganta kiwon lafiyar ga musamman mutanen karkara.
Daga karshe jami’in kungiyar ‘MNCH2 Project’ Yusuf Lawal ya ce sun shirya taron ne domin wayar da kan mutane kan mahimmancin dake tattare da samun inshoran kiwon lafiya.