Gwamnatin Jihar Legas ta Karya farashin shinkafa saboda bikin Sallar Eid-El-Fitr

1

Gwamnatin jihar Legas ta karya farashin buhuhunan shinkafa a jihar saboda sallah eid-El-Fitr da ke tafe.

Kwamishinan aiyukkan goma na jihar Oluwatoyin Suarau ne ya sanar da haka da suke kammala shirye- shiryen fara siyar da shinkafar.

Suarau ya ce hakan zai taimaka wajen samar da abinci wa mutanen jihar musamman yadda kasan ke fama da matsalar koma bayan tattalin arziki.

Ya kuma kara tabbatar wa mutane cewa shinkafar wanda aka rage wa farashi lafiyayya ce.

‘’Farashin da aka sani na shinkafar bai canza ba; babbar buhu mai nauyin kg 50 za a siyar da shi akan Naira 12,000, 25kg akan Naira 6,000 sannan 10kg za a siyar da shi akan Naira 2,500’’.

Aa a samu shinkafar a wurare kamar haka; cibiyoyin kula da kayayyakin aiyukkan noma dake Ojo, Ajah,Odigunya da Epe da kuma Hedikwatan kananan hukumomin jihar.

Sauran wuraren da za a sami shikafan sun hada da Agricultural Development Area Complex dake Oko-Oba a Agege, ma’aikatar lilimi na jihar legas dake Mary land, harabar makarantar Government Technical College dake Idiku- Alikosho da kuma Eko Farmers Mart dake Surulere.

Share.

game da Author