Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da hana harkar sufuri ko na sa kai da Babura tun daga kauyen Kakau har Jere

0

Babban jami’in da ke kula da ayyukan yaki da miyagun ayyuka (Operation Yaki), Kanal Yusuf soja mai ritaya ygwamnati ta dauki mataki ne bayan tattaunawa a majalisar tsaro na jihar da tayi wanda ya samu halarcin sarakuna da kuma hakiman yankin da abin ya shafa.

Yanzu dai an hana amfani da Babura tun daga garin Kakau zuwa Jere dake titin Kaduna zuwa Abuja.
Kanar Yusuf yace duk wanda aka kama yana amfani babur a yankin da aka hana zai dandana kudarsa bayan an kwace babur din.

“Daga kakau zuwa Jere an hana amafani da Babura daga gobe litini. Idan muka kama mutum yana tuka babur za mu kama shi muhukuntashi a matsayin dan ta’adda.

“ Mun gudanar da taro tare da sarakunan yankin cewa su gaya wa mutane duk wanda aka kama ya na amfani da babur za a daukeshi dan ta’adda ne. Saboda mun gano cewa su ‘yan ta’addan suna amfani da babura ne wajen yin garkuwa da mutane da safarar ‘yan ta’adda a cikin garuruwa da dazukan yankin.

“Sannan za mu shiga har cikin dazukan wannan yanki domin kama duk wanda muka gani yana tuka mashin, zamu kwace sannan mu hukuntashi a matsayin dan ta’adda.”

Ya ce dokar za ta fara aiki ne daga garin Kakau zuwa Jere wadanda suke kan babbar titin Kaduna zuwa Abuja, kamar yadda ya bayyana wa BBC.

Bayan haka gidan Jaridar PREMIUM TIMES HAUSA ta nemi ji daga bakin mazauna yankin da abin ya shafa mafi yawa daga cikin mazauna garuruwan sun nuna jin dadinsu akan hakan inda suka ce idan dai hakan zai samar da tsaro a kan titin toh laba’asa.

“ Abu daya da muke rokon gwamnati akai shine su yardan mana mu iya amfani da baburan mu a cikin garuruwan mu da safe wajen zuwa gonakin mu da asibiti. Amma bayan haka tsaro ya fi komai. Muna murna da wannan shiri na gwamnati.” Inji Sani Bariki a garin Jere.

Ita kuma Halima Bala, mai siyar da abinci a garin ta ce lallai mutane za su takuru amma tsaro dai shine yafi komai.

“ A dan daga mana kafa da rana mudan gudar da hidindiminmu saboda duk nan haka karkara ne da Babura ne ake dan gudanar da zirgazirga.”

Share.

game da Author