Gwamnati za ta kafa makarantun Boko na matan Aure

1

Ministan Al’amuran mata Aisha Alhassan ta ce gwamnatin Najeriya za ta kafa makarantun boko na matan aure musamman matan da sukayi aure da wuri kafin kamala karatunsu kuma basu ci gaba ba.

Aisha Alhassan ta ce za su raba makarantun bangarori biyu ne. Daya na matan da suka fara karatu amma aure ko kuma wata matsalar ta hana su kammalawa sannan bangare na biyu kuma na yaki da jahilci.

Ta kuma kara da ce za su tabbatar da sun kafa makarantun koyar da yaki da jahilci wa mata a duk kananan hukumomin da ke kasar nan.

“Duk matan da suka yi aure da wuri za su sami damar samun ilimin boko daga gidajen mazansu ba tare da sun sha wahala ba.”

Daga karshe ta roki shugabanin addini da iyaye da su mara ma wannan shiri baya domin samun nasara wajen samar wa mata Ilimin da suke bukata.

Share.

game da Author