Gwamnati ta amince a siya wa NAHCON ginin Metro Plaza a matsayin ofishinta na dindindin

0

Gwamnatin Najeriya ta amince da a siya wa hukumar kula da jin dadin mahajjata ta kasa NAHCON ofishi na dindindin a Abuja.

Tunda a kafa hukumar a 2006, ta na zama ne a ofisoshin aro. Yau gwamnati ta amince da a siya wa hukumar Metro Plaza.

Gwamnatin ta amince da haka ne ranar Laraba a taron kwamitin zantaswa na mako mako da ake yi a fadar shugaban kasa wanda mukaddashin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya jagotanta.

Shugaban hukumar NAHCON Abdullahi Mohammed ya ce tun da gwamnati ta kafa hukumar a shekaran 2006 take aiwatar da aiyukkanta a ofishin aro.

Share.

game da Author