Fatan Alhairi zuwa ga Hadiza Gabon

0

Hadiza Aliyu Gabon, wacce ta fara fita a finafinan Hausa cikin 2009, a fim din “Artabu”. A yau ta zama abin kwatance, abin alfahari, abin godiya, abin tinkaho kuma uwa, uwar daki da kuma sarauniyar gajiyayyu.

Ba don komai ba sai don irin yadda ta ke sadaukar da lokacin ta da dukiyar ta wajen taimaka wa makwabta da kuma musammam tallafin jin kai da ta ke yawan bayarwa a sansanin ‘yan gudun hijira, wanda ko a kwanan nan sai da ta yi haka a Sansanin ‘Yan Gudun Hijira da ke Wudil, a Jihar Kano.

A wannan lokaci da ake fafutikar nema da tara kudi bakin-rai-bakin-fama, lokacin da yawanci wanda ya samu ko ya dai jida ya tara a banki, ko kuma ya kimshe ko ya maida su kadara, an samu wata matashiyar yarinya da duk da cewa ta na da zafin nema, hakan bai hana ta diba ta na bayarwa ga inda ya dace a bayar ba.

A yau 1 Ga Yuni, 2017 ne Hadiza Gabon ta ke cika shekara 28 a duniya. Gidan Jaridar PREMIUM TIMES HAUSA na taya ki murnan zagayowar ranar haihuwarki.

Share.

game da Author