El-Rufai ya rusa masarautun da Makarfi ya kirkiro a 2001, ya mai da su yadda suke da

0

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da rusa duk wata masarauta da aka kirkiro da ita a 2001. Kwamishinan kananan hukumomi da Masarautun jihar Ja’afaru Ibrahim ne ya sanar da haka da yake ganawa da manema labarai a Kaduna.

Jaafaru ya ce gwamnati tayi hakane bayan nazari da ta yi akan dalilan da yasa gwamnatin Makarfi ta kirkiro sabbin masarautun da kuma ganin irin kudaden da ake kashe wa masarautun yanzu.

Gwamnati ta rusa duk wata masarauta da aka kirkiro a wancan lokaci sannan ta dawo da yadda masarautun jihar suke kafin lokacin.

Yanzu dai an koma Hakimai 77 da dakatai 1,429 kamar yadda suke a can da ba yadda gwamnatin ta gada ba na Hakimai da gundumomi 390 da sarakai da masu Unguwa 5,882.

Kwamishinan yace daya daga cikin dalilan daya sa dole gwamnati ta dauki wannan mataki shine ganin irin kudaden da take kashe wa sabbin masarautun da babu gaira babu dalili sannan kuma gashi babu wasu ababen more rayuwa da aka samar wa mutanen jihar.

“Duk da cewa gwamnati na iya kokarinta wajen biyan sarakan da aka nada kananan hukumomi sun kasa biyan Hakimai da dakatai dake kananan hukumominsu.

“ Zazzau na da gundumomi na masarautu guda 86 inda Kano da tafi yawan mutane da kananan hukumomi ke da 44, katsina kuma 33.

“Sarakuna za su turo sunayen mutane uku domin zaben sabon Hakimai a masarautun da aka dawo dasu yadda suke ada.”

Karanta labarin a shafin mu na Turanci: In major restructuring, El-Rufai slashes Kaduna districts to pre-2001 numbers

Share.

game da Author