A yau Talata ne gwamnatin Jihar Bauchi ta sanar da kashe sama da naira Miliyan 96 wajen siyan dawakai wa masarautu shida dake fadin jihar.
Kwamishina kananan hukumomin jihar Nasuruddeen Mohammed ne ya sanar da haka da yake zantawa da manema labarai a A Bauchi.
Ya ce masaurun da aka siya wa dawakan sun hada da Bauchi, Misau, Dass, Jamare, Katagum da Ningi.
“ Wannan gwamnati ta kashe naira Miliyan N96 wajen siyan dawakai ga masarautun jihar shida. Gwamnatin jihar tayi haka ne domin kara bunkasa al’adun gargajiya a jihar.
A wani rahoto na majalisar dinkin duniya da ta fitar a 2015, jihar Bauchi dai na daya daga cikin jihohin da suka fi yawan mutanen dake fama da talauci a kasa Najeriya.
Rahoton ya nuna cewa kasha 86.6 na mutanen jihar Bauchi na fama da talauci.
Bayan haka kuma kwamishinan yace gwamnatin jihar ta kashe sama da naira Miliyan 72 wajen yi wa duka kananan hukumomin jihar takardun shaidar zama dan jihar na bai daya. Sannan kuma gwamnati ta kashe miliyan 55 wajen buga risit wa duka kananan hukumomin jihar.
Discussion about this post