Dole ayi kaffakaffa da yadda baragurbin likitoci ke kara wa marasa lafiya jini ba tare da suna bukata ba – Likitocin jihar Zamfara

0

Kungiyar likitocin Najeriya reshen jihar Zamfara ta koka kan yadda ma’aikatan kiwon lafiya a jihar ke kara wa mutane jini a asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya ba tare da an tabbatar da ingancin jinin ba.

Sakataren kungiyar Mannir Bature ya yi tir da hakan a lokacin da kamfanin dillancin labaran Najeriya ta yi hira da shi a Gusau.

“Mun yi kokarin bin didigin wannan matsalar a asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya a jihar inda muka gane cewa mutane da dama snu rasa rayukansu ta dalilin karin jini”.

Mannir Bature ya ce an sami akasi kan haka ne saboda wasu ma’aikatan kiwon lafiya da basu kware a akinsu ba sai kawai su kara wa mutane jini a lokacin da bai kamata ba.

“Wasu ma’aiktan kiwon lafiya na kara wa marasa lafiya jini batare da sun tabbatar ko yana bukata ba”.

“Karancin na’urorin gwajin jini na daya daga cikin matsalolin da ke sa ma’aikatan kiwon lafiya ke bada jini da bai dace da wanda ke bukata ba musamman wanda ke dauke da wata cuta”.

Ya shawarci gwamnatin tarayya da ta bude cibiyyar gwada jini a kalla daya a kowane mazaba uku dake jihar.

Ya ce a yanzu haka na’urorin gwajin jini da ke fadin jihar Zamfara biyu ne kawai wanda daya ke asibitin Yariman Bakura dake Gusau sannan daya na asibitin MSF dake Anka.

Mannir Bature ya shawarci kwararrun ma’aikatan asibiti da su tabbatar da cewa ma’aikatan da ke yi wa mutane karin jini sun tabbatar da ingancin jini kafin a kara wa mutum.

Share.

game da Author