Sanata mai wakiltar Kogi ta yamma Dino Melaye ya tsallake rijiya da baya yau bayan hari da wasu dauke da bindiga da ba’a san ko su waye ba su ka far ma wani taron gangami da ya shirya domin nuna adawarsa ga gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello.
Dino tare da wadansu magoya bayansa sun gudanar da zanga zangar ne a garin Lokoja inda suka yi ta kiran gwamnan jihar Yahaya Bello da muggan sunaye.
Bayan sun taro a kofar Kwalejin kimiyya da fasaha mallakar jihar Kogi sai wasu da ba’a san ko su waye ba suka far ma taron suna harbe harbe da bindigogi inda har hakan yayi sanadiyyar mutuwar mutane biyu, daya daga cikinsu dalibin Kwalejin.
Jamian tsaron da suke kare sanata Dino suma sun sami raunuka a jikkunansu.
Bayan mintoci kadan sai gwamnan jihar Yahaya Bello ya ziyarci wurin da abin ya faru inda ya umurci jami’an tsaro da su tabbata sun gudanar da bincike akan hakan.
Karanta labarin a shafin mu na turanci a nan: Two feared dead as Dino Melaye survives attack