Dalilai Biyar da ya sa cutar Sankarau ta yi ta yaduwa a Arewacin Najeriya

0

Mafi yawa da ga cikin mutanen da suka rasa rayukansu a sanadiyyar bullowar cutar Sankarau mazauna arewacin Najeriya
Bisa ga bayanan da ya fito daga hukumar kula da hana yaduwar cututtuka na kasa NCDC sun nuna cewa jihohin yankin arewacin kasa Najeriya wanda ya hada da Kano, Zamfara, Kebbi da Yola sun yi fama da cutar inda mutane 1,114 suka rasa rayuwarsu a sanadiyyar kamuwa da cutar.

Wata likitan da take aiki da likitocin da suke bada agajin gaggawa a kasa Najeriya mai suna Miriam Alia ta ce rashin sani kan cutar daga bangaren mutane da kuma ma’aikatan asibiti na cikin dalilin da ya mutane da dama suka rasa rayukansu.

Idan ba a manta ba gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari wanda jihar shi ce ta fi samun yawan mutane da suka rasa rayukansu ta dalilin cutar ya taba cewa bullowa da yaduwar cutar yana da nasaba ne da irin laifukan da mutane sukeyi wa Allah. Wanda hakan baiyi wa mutane da yawa dadi ba inda ya raddi musamman daga sarkin Kano Muhammadu Sanusi.

Dalilin hakan ne ya sa Miriam Alia ta bada bayanai akan dalilin da ya sa yankin arewacin Najeriya din ke yawan fama da cutar sankarau domin wayar da kan mutane.

Ta ce:

1. Yanayin iskan da yakin arewacin Najeriya ta ke da shi wanda ke iya daukan kwayar cutar sankarau daga yawun wanda ke dauke da cutar ta kuma yada wa sauran mutane musamman a lokacin rani yakan sa cutar tayi ta yaduwa.

2. Karancin alluran rigakafin cutar musamman wanda ke kashe kwayar cutar da ya adabi mutane a wannan shekaran wanda ake kira da Meningitis C.

3. Daukan tsawon lokacin sarrafa wannan alluran rigakafin wato Meningitis C vaccine.

4. Rashin wayar da kan mutane kan mahimmancin tsaftace muhali da kuma kwana a dakin dake da issashen isaka sannan kuma da sanar dasu illolin dake tattare da rashin yin hakan.

5. Tsadan sarrafa wannan alluran rigakafin cutar sankarau wanda ake kira da Meningitis C da kuma rashin iya ajiye maganin na wani tsawon lokaci ba

Share.

game da Author