Dalilai 6 da ke hana mutane taimakawa da jininsu a asibitocin Najeriya

0

Faith Ajani, babban likita ne kuma jami’i a kungiyar ‘Blood Drive Initiative’ ya yi kira ga mutanen Najeriya da su yawaita bada gudunmawar jini domin ceto rayukar mutanen dake bukata.

Ajani ya fadi haka ne ranar Laraba a wajen taron tunawa da ranar bada gudunmawar jini da ake yi kowace shekara Abuja wanda ke da taken ‘’Me za/ki iya yi? Taimaka da jini. Bada jini yanzu. Bada jini lokaci lokaci’’.

A hirar da gidan jaridar PREMIUM TIMES ta yi da shi, ya ce an shirya taron ne domin a wayar wa mutane da kai kan mahimmancin bada gudunmawar jini domin ceto rayuwar mutanen musamman ganin yadda ake yawan samun hadarori da ababen hawa da jinin da mutane kan rasa idan tsautsayin hare-haren kungiyar ‘yan ta’adda ya hada da su.

Ajani ya ce bayan taimakawa mutane masu matsaloli irin haka, ba da gudunmawar jini na taimakawa wa likitoci a lokacin da suke fida sannan kuma ya na taimakawa mata wajen haihuwa.

Likitan ya koka da yadda mafi yawan asibitocin Najeriya ke fama da karancin jini a ma’ajiyar jinin su wanda kafin a sami jinni a lokutta da dama sai an biya ko kuma dan uwan mara lafiyar na bukata sai a fita nema hurjanjan.

Ya ce hakan na faruwa ne saboda rashin sanin muhimmancin bada jini, da jiyeshi har zuwa lokacin da za a bukata.
Ya ce babbar dalilan da ke hana mutanen Najeriya bada jini sun hada da

1 – Rashin sanin muhimmancin bada jini, da jiyeshi har zuwa lokacin da za a bukata.

2 – Zato da masu bada jini keyi na siyar wa matsafa Jininsu.

3 – Mutumin da ya fito musamman daga yankin Arewa ba su yardasu bada jininsu hakan kawai ba wai don kila a bukata nan gabasaboda yarda da suke dashi cewa ciwo jarabawace daga Allah abari har sai bukatar hakan ya taso tukuna sai a nemi yin haka.

4 – Mutumin da ya fito musamman daga yankin gabacin kasar bai damu da ko ya bada jini ba ko a a shidai yaji ammai a aljihunsa kawai. Ko ya akeso ma zai yi.

5 – Mutumin da ya fito musamman daga kudancin kasar kuwa ya danganta bada jini da addininsa domin wasu cikin su sunce addininsu ya haramta musu bada jininsu kad’an.

6 – Rashin wayar wa mutanen karkara da kai akan muhimmancin taimakawa marasa lafiya da jini.

Share.

game da Author