Coci a Kaduna ta raba abincin buda baki ga daruruwan musulmai a jihar

0

Kamar yadda ta saba duk shekara Cocin ‘Christ Evangeligal Intercessory Felloship Ministry’ dake Sabon Tasha Kaduna ta kan rabawa masu Azumi abincin bude baki a jihar Kaduna, wannan shekarar ma cocin ta yi haka inda ta raba abincin bude baki ga masu Azumi sama da 500 a unguwannin jihar.

A makon da ya gabata ne wasu daga cikin mazauna garin Kaduna su kayi kira ga gwamnatin jihar da ta agazawa masu Azumi ganin yadda mutane ke fama da wuyar rayuwa.

Duk da cewa gwamnati ba ta amince da wannan kuka da kira na jama’a ba kungiyoyi da dama sun fito domin taimakawa mutane da abincin buda baki.

Babban Faston cocin Yohanna Buru ya ce suna yin haka ne domin taimakawa ‘yan uwa musulmai a wannan wata na Ramadan.

”Ya zama dole mu taimaka wa ‘yan uwan mu da suke azumi musamman yadda kayyayakin abinci ya yi tsada a kasuwa kuma yin hakan zai karfafa dangantakar da ke tsakanin musulmai da Kiristoci a jihar da samar da zaman lafiya a tsakanin mu gaba daya”

Ya kuma yi kira ga ‘yan kasuwa musamman wadanda suke kara kudaden abinci da na masarufi a lokacin azumi da su gujewa yin hakan. Sannan ya yi kira ga attajiran kasar nan da su dinga kokarin agaza wa talakawa musamman marayu da wadanda basu da shi.

Wani cikin wadanda suka amfani da wannan tallafi Wambai Isa ya jinjina wa Yohanna Buru da Cocin sa kan wannan aikin taimako da suka saba yi musamman a wannan lokaci da rayuwa tayi tsada.

Share.

game da Author