CIWON SIGA: Abubuwa 5 da mai fama da ciwon Siga zai kiyaye a lokacin Azumi

0

Bincike ya nuna cewa rashin cin abinci akan lokacin na da matukar illa ga wanda ke fama da ciwon siga amma hakan ba shine zai sa mutum yaki yin Azumin ba.

Wani kwararren likita mai suna Amadi Ikechukwu dake aiki a babbar asibiti mallakar gwamnatin Tarayya wato ‘Federal Staff Hospital’ a Abuja ya ce masu fama da cutar siga za su iya azumi amma akwai sharudda.

Ga sharuddan:

1. A yawaita yin gwaji fiye da yadda ake yi da saboda gane tashin ciwon da wuri.

2. A tabbatar ana cin abincin da ya kamata musamman abincin da zai kara karfi a jiki a lokacin bude baki da kuma suhur wanda ya hada da ‘Brown Rice’ wato shinkafan da masu fama da cutar ke ci, buredin da aka yi ta da alkama, tuwon alkama, cin ganyayyakin da ake ci, shan ‘ya’yan itatuwa da kuma sauransu.

3. Za a iya shan kayan zaki amma ba kullum ba.

4. Mutum zai iya cin kifi, wake da naman kaza ko ta Sa.

5. A tabbatar ana ziyartar asibiti akai akai domin ganin likita.

Share.

game da Author