Buhari na mika sakon gaisuwarsa ga ‘yan Najeriya – Aisha Buhari

0

Uwargidan shugaban Kasa Aisha Buhari ta sanarwa ‘yan Najeriya cewa shugaban kasa na samun Lafiya kamar yadda ya kamata.

Aisha ta fadi haka ne a filin jirgin saman Abuja da ta dawo duba lafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari da yake kasar Britaniya ganin likitocinsa.

Aisha ta ce Buhari na samun lafiya kuma ya na mika sakon gaisuwarsa da godiyarsa ga ‘yan Najeriya bisa addu’oin da suke ta yi masa.

Bayan haka kuma ya jinjina wa mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo kan yadda ya ke gudanar da mulkin kasa.

Share.

game da Author