Hukumar Alhazai ta Kasa na sanar da cewa, abu wani boye-boye ko nuku-nuku dangane da kudin tafiya aikin Hajjin bana. Shin ta yaya mu ka kai ga farashin kowace kujera ne? Mun yanke farashin karamar kujera, matsakaiciya da kuma kudin babbar kujera, bayan mun cimma matsaya tsakanin hukumar mu da jihohi da kuma sauran hukumomin gwamnati masu ruwa da tsaki da ke da alhaki wajen kayyade komai a wannan bangare.
Misali a dauki farashin tikitin jirgin sama. Ba Hukumar Alhazai ta Kasa haka kawai ta zauna ta kayyade kudin tikitin jirgin kowane maniyyaci ba. An zauna an kayyade kudin tikiti ne bayan sake yin yarjejeniya tsakanin Hukumar Alhazai ta Kasa da kuma kamfanonin jiragen da za su yi jigilar maniyyata. Wadanda su ka kayyade wannan kudin tikiti kuwa sun hada da wakilan dukkan hukumomin harkokin sufurin jiragen sama da kuma hukumomin kula da jin dadin Aljazai ta jihohi.