Babbar Kotun Daukaka Kara ta Tarayya da ke Abuja, ta sallami wani da ake zargin dan kungiyar Boko Haram, mai suna Usman Abubakar, wanda aka tsare kimanin shekaru shida.
Shi dai Abubakar, ya shiga hannu ne bayan an kama shi tare da wasu mutane da ake zargi su shida.
An zarge su ne da laifin arcewa tare da yin garkuwa da wasu Turawa bakwai a dajin jihar Bauchi, cikin watan Fabrairu, 2013. An kuma tabbatar da cewa an kashe wadanda aka sace din a cikin Dajin Sambisa, jihar Barno.
Sauran wadanda aka yi wa cajin laifin kisan sun hada da Mohammed Usman wanda aka fi sani da Khalid Al-Barnawi, Mohammed Bashir Saleh, Umar Mohammed Bello wato Abu Azzan.
Akwai kuma Mohammed Salisu, Yakubu Nuhu da kuma wata mata mai suna Halima Haliru. Dukkan su an gurfanar da su ne a kan cajin laifuka 11 da ake tuhumar su da aikatawa.
Yayin da,aka koma sauraren karar, mai gabatar da kara Lawan Sha’aibu da ya bayyana wa kotun cewa ba shi da wata hujja game wanda ake zargin na shida.
Mai gabatar da kara ya nemi kotu ta kara jinkirta masa domin ya kara gurfanar da wasu da ake zargin aikata kisan gillar tare.
Shi kuma lauyan wanda kotu ta wanke ya yi kira da a gaggauta kammala wannan shari’a. Shi kuma mai shar’a John Dantsoho, nan da nan ya sallami wanda kotun tasa ta wanke, sannan ya daga karar zuwa 19 Ga Yuni, 2017.