Gamayyar wasu bankuna a bisa jagorancin Access Bank PLC, wasu bankuna kasar nan da na kasashen waje, sun kwace kamfanin wayar selula na Etisalat, tun daga ranar 15 Ga Yuni, 2017.
Wannan kwace kamfanin Etisalat da a ka yi, ya biyo bayan kasa cimma wata yarjejeniya da aka yi tsakanin kamfanin sadarwa na EMTS, na tsohon shugaban bankin UBA, Hakeen Bello-Osagie tare da wadannan bankuna.
Premium Times ta gano cewa bashin naira bilyan 541 ne ta rike wuyan kamfanin Etisalat, har ya kai aka kwance masa zani a kasuwa.
Babban Kamfanin Etisalat da ke Abu Dabi, hedikwatar Hadaddiyar Daular Larabawa ne ya bayar da sanarwar karbar kamfanin Etisalat na Nijeriya da bankunan suka yi. Ya yi wannan sanarwa ne a ranar Talata.
Tun cikin 2016 ne kamfanin Etisalat ke cikin matsin-lambar neman ya biya ashin naira bilyan 541 wanda kamfanin ya ciwo a wadannan bankuna daban-daban a cikin 2015.
An ce Etisalat ya ciwo basussukan ne da nufin inganta karfi da nisan zangon sa da kuma gyara kayayyakin aikin sa. Tun cikin 2016 kuma wadannan bankuna suka yi barazanar kwace kamfanin, ganin cewa akwai tabbatattun hujjojin da ke nuna cewa bashin ya zama alakakai, Etisalat ba zai iya biya ba.
Ganin haka ne tun a lokacin sai Hukumar Sadarwa ta Najeriya da kuma Babban Bankin Najeriya, CBN, suka shiga tsakani a lokacin, suka roki bankunan da aka tsara lokutan da Etilasat za ta rika biya har a warware.
Idan ba a manta ba, cikin makon jiya, Premium Times ta ruwaito cewa kamfanin Etisalat ya rufta cikin harkallar dimbin basussuka, har kamfanin Mubadala, wanda shi ne abokin hadin guiwar sa na Adu Dabi na dab da janewa daga hadin guiwar da su ke yi.
Discussion about this post