Shugaban Jam’iyyar PDP bangaren Makarfi, Ahmed Makarfi ya musanta yawan mutanen da Jam’iyyar APC tace sun canza sheka a jihar a makon da ya gabata.
Tsohon shugaban jam’iyyar PDP a jihar Kebbi da wadansu magoya bayan jam’iyyar 25,000 ne suka canza sheka zuwa jam’iyyar APC.
Shugaban jam’iyyar Bello Doya ne ya jagoranci masu canza shekar.
Gwamnan jihar Abubakar Bagudu da wadansu ‘ya’yan jam’iyyar daga kananan hukumomi 21 ne suka karbe su a wata kwarya-kwaryar buki da akayi a Birnin Kebbi.
A jawabinsa gwamnan jihar yayi maraba da da su sannan yace jam’iyyar APC za ta yi aiki da su kamar kowani dan jam’iyyar.
Mai magana da yawun masu canza shekar Isah Argungu ya ce gaba dayansu sun canza sheka ne zuwa jam’iyyar APC saboda kyawawan aiyukan da gwamnatin jihar da na kasa ke yi wa mutanen da suka zabe su.
Duk da hakan Makarfi ya ki amincewa da wannan alkalumma da aka bayar na yawan mutanen da akace wai sun koma jam’iyyar APC din a jihar Kebbi domin ya ce a saninsa fadar dakin taro na fadar gwamnatin jihar Kebbi din zai iya daukan mutane 5000 ne kawai ba 25,000 kamar yadda akace wai sun halarci bukin sauya shekar.
Makarfi dai bai bada adadin yawan mutanen da suka canza shekar ba ko da ya fadi hakan.
Bayan haka sakataren jami’yyan PDP na jihar Kebbi Ibrahim Arzika Bui, a hirar da yayi da wannan gidan jarida ta wayar tarho ya ce ba zai canza sheka ba.
‘’Na shiga jami’yyar PDP tun a shekaran 1998 kuma ban taba tunanin canza sheka zuwa wata jami’yya ba. Saboda hakan canza shekar da wasu cikin mu suka yi bai dadani da kasa ba ko kadan.”