Kakakin majalisar Dokokin jihar Kano Kabiru Rurum ya karyata rahoton wata gidan Jarida da ta rubuta wai ya karbi cin hancin naira miliyan 100 domin ya tilastawa majaisar ta dakatar da ci gaba da binciken Sarkin Kano Muhammadu Sanusi.
Rurum ya ce hakan ba gaskiya bane sannan kuma zai kafa wata kwamiti a majalisar da zata binciki wannan korafi.
Ya ce idan har aka fara binciken dole sai wannan gidan jarida da ta ruwaito labarin ta bayyana a gabanta.
Ya ce irin haka shiri ne na makiyansa amma babu kamshin gaskiya a cikinta.
Mukaddashin shugaban Kasa Yemi Osinbajo da wadansu jiga-jigan ‘yan Najeriya ne suka roki majalisar ta gwamnan jihar Abdullahi Ganduje domin majalisar ta dakatar da binciken.