Bai kamata shugabannin kasa su rika nada shugaban hukumar zabe, INEC ba -Jega

0

Tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa, Farfesa Attahiru Jega, ya bayyana ingancin hukumar zabe zai karu ainun matukar aka ce ofishin shugaban kasa tsai tsame hannnun sa daga ikon nada shugaban hukumar.

Jega ya yi wannan jawabi jiya Litinin, a wurin wata lacca da aka shirya a Cibiyar Nazari da Binciken Dimokradiyya, Gidan Mambayya, Kano. Ya ce za a iya cimma wannan manufa idan aka kafa doka a kai,
Farfesan ya nuna muhimmancin samar da hukumar zabe mai zaman kan ta, ta kasance ba bu ruwan fadarc shugban kasa da samar mata kudade ko kuma nada mata shugaba.

Ya kuma nuna damuwar sa ganin yadda kwamitin Mai Shari’a Lawal Uwais ya bada shawarar cewa ya kamata a ba INEC wuka da naman ikon nada shugaba da kwamishinoni, amma sai bangaren zartaswa bai amince da hakan ba. Amma har yau, ku lura cewa ahugaban kasa ne ke nada shugaba da kwamishinonin hukumar zabe ta kasa.

Sai dai kuma ya tabbatar da cewa shugaban hukumar na yanzu, ya na cin gashin da ya kamata ya samu ba tare da yin dogaro daga wamiti ba, kamar dai yadda kwamitin Uwais ya ce a yi.

Share.

game da Author