Ba za mu zuba Ido mu bari wasu na yin furucin da ka iya ta da zaune tsaye a kasarnan ba – Yemi Osinbajo

0

Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya ce gwamnati ba za ta saka ido ta bari kungiyoyi ko wasu mutane na yin maganganun da zai iya tada zaune tsaye a kowani sassa na kasar nan ba.

Osinbajo ya fadi haka ne da yake ganawa da shugabannin dattawan Arewa da suka kai masa ziyara a fadar gwamnati.

Ya ce dole ne gwamnati ta kara tsaurara matakai akan hakan domin gujewa barkewar tashin-tashin din da ba a shirya masa ba.

“ Yanzu da zarar rikici ta barke kawo karshen ta sai Allah kuma na sani cikin ku babu wanda yake so ace wai hakan ya faru ko da da makiyinsa ne.”

“ Ina kira ga duk ‘Yan Najeriya da mu zo mu hada hannu domin ganin munciyar da kasarmu gaba duk da banbance-banbancen kabila da asali da muke dashi.”

Ya umurci dattawan arewan da su isar da wannan sako ga ‘yan Arewa.

Share.

game da Author