Godiya ta tabbata ga Allah mai Girma da daukaka, Mai kamala a cikin sunayensa, Allah ya kara tsira da aminci ga shugabanmu AnnabiMuhammadu da iyalansa da sahabbansa baki daya.
Babu shakka an umurci musulmi da ya lizimci Ibada, ya tsare dokokin Allah. Hakan zai tsarkake zuciyar sa. Allah ya shar’anta Ibadu kala-kala, na Wajibi da na Nafila kamar azumi.
Azumin Sittu Shawwal wata zinariyar garabasa ne da Allah ya azurta wannan al’uma da shi. Annabi Muhammadu (SAW) ya kwadaitar da yin azumin kwanaki shida a cikin watan Shawwal bayan anyi azumin watan Ramadan. An karbo daga Abu Ayuba (R.A) cewa Annabi Muhammadu (SAW) ya ce: wanda ya azumci Ramadana kuma ya bi bayan sa da azumin kwanaki
shida daga Shawwal, to, kamar, ya yi azumin shekara ne.
Yin azumin kwana shida bayan Ramadana, a cikin watan Shawwal, yana nuna godiyar bawa ga ubangijin sa, ga falalar da ya yi masa na yin azumin Ramadana, kuma kokarin yawaita ayyukan alhairi ne da biyayya ga Allah a cikin bauta. Bugu da kari ga lada mai yawa, kamar ladan azumin shekara daya.
Yana daga cikin falalar azumin shawwal, cike gibin da nakasun da bawa ya samu a cikin azuminsa na Ramadana. Kuma alama ce da ke nuna karbuwan azuminsa na Ramadana.
SHIN YA HALATTA GABATAR DA AZUMIN KWANA SHIDA NA SHAWWAL KAFIN RAMAKON AZUMIN RAMADANA GA WANDA YA SHA AZUMIN RAMADANA?
Babban Malami Sheikh Abdulaziz Bin Bazz ya ce : abinda ya fi dacewa shin ne rama azumin Ramadana ga duk wanda ya sha azumin kafin ya fara azumtar kwanaki shidan Shawwal. Sabo da rama azumin Ramadana Wajibi ne, azumin kwanaki shidan na Shawwal kuma Nafila ne. Shari’a na gabatar da aikin Wajibi akan Nafila. Kuma a hadisin da ya gabata ance ne wanda ya azumci Ramadana kuma ya bi bayan sa da azumin kwanaki shida daga Shawwal, to, kamar, ya yi azumin shekara ne. Kaga idan mutum bai kammala azumin Ramadana ba, kafin fara azumin kwanaki shidan Shawwal, to, be yi amfani da hadisin ba, kuma be cika ka’idar garabasar ba.
Ana fara azumin kwana shidan Shawwal bayan Sallah da kwana biyu, an samu a yi su a jere cikin kwana shida, ko a rarrabe duk yanda ya saukaka, a cikin kwanakin Shawwal. Sannan ba laifi ba ne mutum ya yi azumin kwana daya, ko biyu, ko kuma abinda ya saukaka gwargwadon ikon sa, ga wanda ba zai iya yin azumin kwana shidan ba.
Allah ya bamu ikon yin kyawawan ayyukan da za su kusantar damu zuwa gareshi, kuma ya bamu ikhlasi, sannan ya karbi ibadunmu. Amin.