Masarautar Lamidon Adamawa ta nada tsohon mataimakin shugaban Kasa Atiku Abubakar sabon Wazirin Adamawa.
Jami’in da ke hudda da jama’a na masarautar Muawiyah Abba ne ya sanar da haka.
Ya kara da cewa an nada dan Atiku Abubakar, Aliyu Atiku Abubakar sabon Turakin Adamawa wanda sarautar ubansa ne kafin zama wazirin Adamawa.