‘Yan sandan Jihar Ogun na neman wani mutum da ake zargin ya guntule yatsan ‘Yar sa mai shekaru 14, saboda haushin ta ki zuwa ta aske irin kitson da ta yi, bayan ya ba ta naira 100 ta je ta yi askin.
Wata kungiyar sa-kai wacce ta kai rahoton faruwar hakan, ta ce yarinyar dai ta na shirye-shiryen rubuta jarabawar kammala karamar sakandare a lokacin da al’amarin ya faru, mahaifinta Musa Olayinka ya datse mata yatsa.
Wannan ta’asa ta faru ne a garin Ijebu-Ode, kuma kungiyoyin sa-kai ciki har da Child Protection Network sun shiga cikin lamarin.
Shugaban kungiyar Kunle Sanni, ya shaida wa Premium Times cewa kungiyar sa na aiki tare da hadin kan jami’an ‘yan sanda domin a Kano kuma a hukunta mahaifin yarinyar, wanda tun bayan guntule mata yatsa ya tsere.
“Mun hadu da yarinyar ne a wacce a yanzu kamata ya yi a ce ta kammala karamar sakandare, mu ka gan ta da guntulallen yatsan hannun hagu, da kuma raunuka a jikin ta. Saboda mahaifin na ta ya sa igiya ya daure ta kuma ya rika zabga mata bulala.”
“Yarinyar nan marainiya ce, uwar ta ta mutu, sai kishiyar uwar ta muka samu, amma mahaifin na ta ya tsere. Kawai don ya ba ta N100 ta yi aski amma ba ta yi ba, shi ne ya guntule mata yatsa.”
Kakakin ‘yan sanda Abimbola Oyeyemi, ya ce za su yi kokarin kamo mahaifin domin kotu ta hukunta shi.