An zabi wasu cibiyoyin kiwon lafiya biyu a karamar hukumar Suletankarkar don yin aiki na awoyi 24 kullum

0

Karamar hukumar Suletankarkar dake jihar Jigawa ta zabi wasu cibiyoyin kiwon lafiya biyu domin samar da ingantacciyar kiwon lafiya ba kakkautawa a garuruwan Suletankarkar da Danzomo.

Shugaban sashen hulda da jama’a na karamar hukumar Dauda Sulaiman ne ya sanar da haka da ya ke zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Dutse ranar Alhamis.

Shugaban cibiyoyin kiwon lafiya na karamar hukumar Abdullahi Maigatari ne ya sanar da hakan a lokacin da suka tattauna da ma’aikatan bada alluran rigakafin cutar shan inna.

Maigatari ya ce hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya na jihar Jigawa PHCDA na kokarin ganin ta samar da ingantattun kayayyakin aiki da ma’aikatan da za su yi aiki ko da yaushe a wannan asibitocin.

Shugaban bangaren ruwa da tsafta na karamar hukumar WAHS Wada’u Sulaiman ya jinjinawa ma’aikatan bada alluran rigakafin cutar shan inna da sauran masu ruwa da tsaki a yankin akan kokarin da ake yi wajen kammala bada alluran rigakafin cutar a yankin.

Daga karshe mai rikon kwaryan shugabancin karamar hukumar Suletankarkar Haladu Bulama ya mika godiyarsa ga hukumar PHCDA na jihar kan kokari da ta keyi wajen samar nagartacciyar kiwon lafiya a yankin.

Share.

game da Author