Fulanin dake kauyukan karamar hukumar Sardauna a jihar Taraba sun yi kira ga mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo da ya kawo musu dauki kan kisan da ake yi musu.
Fulanin sun ce shugaban karamar hukumar Sardauna John Yep ne ya turo wasu ‘yan daban da suke ta yi musu kisan kiyashi a kauyukan.
A bayanin da wasu datawan kauyuka hudu suka bayar a ranar Laraba sun ce rikicin ya fara ne a lokacin da ‘yan daban suka fara yin zanga-zanga domin jami’an tsaro sun kama wani shugabansu mai suna Umaru CID dake garin Nguroje.
Sun kuma ce jami’an tsaron sun kama Umaru CID ne saboda shari’ar da ake yi akan wani fili.
‘’A ranar 16 gawatan Yuni ‘yan sanda suka shigo garin Nguroje da asuba suka kama wasu shugabanin ‘yan ta’adda da ake zargin su da tada zaune tsaye a garin’’
‘’Da jin hakan sai shugaban karamar hukumar Sardauna John Yep ya aiko wasu matasan garin Mambila zuwa Nguroje akan cewa a ta dalilin Fulanin dake wurin ne aka kama wadanan mutanen wanda hakan ya tada rikicin da ya hana shiga da fita a garin Nguroje da wasu garuruwan da kekusa da su’’.
Kakakin rundunan ‘yan sandan jihar Taraba David Misal ya sanar wa manema labarai a jalingo cewa rikicin ya samo asaline tun bayan kama wani mazaunin garin Mambila da wata kotu ta sa ayi inda aka kaishi kurkuku.
Ya ce ‘ya’yan wannan mutumin da kotu ta bada umurin a kama ne suka je gidan makiyayin da ya kai mahaifinsu kara kotu wato Riwi Ahmadu suka yimasa barazanar hallakashi idan bai sa an saki mahaifinsu ba.
‘’Da bafulatanin ya yi watsi da barazanarsu sai yaran mutumin suka bankawa gidan Riwi Ahmadu wuta sannan suka ji masa rauni i’’.
Misal ya ce a yanzu haka sun tura jami’an tsaro da dama a wurin sannan kwamishan ‘yan sandan ya dauki nauyin bin didigin dalilin rikicin.
‘’Mutane bakwai suka rasa rayukansu a dalilin wannan rikici sannan gidaje da laanta dukiyoyi masu yawa.”
Osinbayo ya umarci Sifeton ‘yan sanda da aika jami’an tsaro yankin sannna a tabbata an kawo karshen wannan rikici.