Hukumar kula da siyar da ingantattun magunguna ta kasa da kasa UNITAID na shirin shigo da sabuwar maganin cutar kanjamau wanda zai taimaka wajen kara karfin garkuwar jikin masu dauke da cutar da magungunar da suke amfani da su a baya baya musu aiki.
Kamfanin sarrafa magunguna mai suna ViiV Healthcare da ke karkashin kamfanin GlaxoSmithKline ne ta kirkiro wannan maganin mai suna Dolutegravir (DTG).
Gwamnatin Amurika a shekaran 2013 ta fara gwada maganin akan mutane 20,000 a kasar Kenya sannan ta amince a shigo da shi a kasashen Najeriya da Uganda.
Hukumar UNITAID ta ba da bayanai cewa mutanen da ke dauke da cutar kanjamau a kasashen da suka ci gaba za su iya zaban amfani da wannan sabuwan maganin DTG din musamman mutanen da ba su taba shan maganin cutar kanjamau ba da kuma wadanda maganin cutar kanjamau ya ki aiki a jikin su.
Wata darektan jami’ar kirkirowa da sarrafa magunguna ‘Mary Land School of Medicine’ a kasar Kenya Sylvia Ojoo ta ce kashi 15 bisa 100 na mutanen da ke dauke da cutar kanjamau na fama da matsalar rashin aikin maganin cutar a jikinsu a kasar Kenya.
Amma wata mazaniyar kasan Nairobi Doughtiest Ogutu wace ta fara amfami da maganin DTG ta ce ta daina sammun mugayen mafarkai sannan kuma yadda take cin abinci ya karu yanzu.
Ta kuma kara da cewa maganin ya rage yawan kwayoyin cutar kanjamau a jinin ta daga 450,000 zuwa 40,000.
Daga karshe shugaban hukumar kula da yaduwar cutar kanjamau da cututtukan da ake kamuwa da su ta hanyar juma’I na kasar Kenya Martin Sirengo ya ce kasar Kenya na da mutane miliyan 1.5 da ke dauke da cutar kanjamau sannan kadan daga cikinsu ne kadai ke samun maganin cutar.