Wasu masu yin garkuwa da mutane sun yi garkuwa da wani matashin dan kasuwa mai suna Abubakar Kalirko a garin Kakirko dake karamar hukumar Wurno, Jihar Sokoto.
Kamar yadda shugaban rundunar ‘Civil Defence’ na jihar Babangida Abdullahi ya sanar wa manema labarai ya ce barayin dai sun biyo Abubakar ne har gida sannan suka dauke shi a gaban iyalinsa.
Masu garkuwan sun bukaci da a biya naira 500,000 domin fansan Abubakar.
Jami’an tsaro sun bazo domin gano inda Abubakar ya ke boye domin kwato shi daga hannun barayin.