An nada Ahmed Musa Sardaunan Matasa a Kano

0

Jiya Alhamis ne wata kungiyar dalibai da ke Kano ta nada Ahmed Musa, sarautar jagaban matasan Arewa a Kano.

Ahmed Musa dai ya na buga kwallonsa ne a kungiyar kwallon kafa na Leicester City dake kasar Britaniya.

Matasan sun ce sun karrama Ahmed Musa ne saboda nuna masa cewa matasan Arewa na tare da shi.

Makonni Biyu da suka wuce Ahmed Musa ya sake yin Aure na biyu bayan ya rabu da matarsa ta farko wato Jamila.

Bayan haka kuma ya bude wani gidan motsa jiki a Kano.

Share.

game da Author