An mika takardun yi wa Sanata Dino Melaye Kiranye

0

Hukumar Zabe ta Kasa ta karbi takardun shaidar rattaba hannu da mutanen mazabar Sanata Mai wakiltan Kogi ta Yamma Sanata Dino Melaye suka mika yau a ofishinta.

Kamar yadda doka take, akalla sai kashi 50 bisa 100 na Mutanen mazabar dan majalisar sun saka hannu a kiranyen kafin hakan iya tabbata.

Yanzu dai an sami kashi 52.3 wanda ya kama mutane dubu 188,588 ke nan na mutanen Kogi ta yamma da suka saka hannu akan sai ya dawo.

Ko da yake sanata Melaye ya ce wanna shiri na yi masa kiranye, shiri ne wanda gwamnan jihar Yahaya Bello ya shirya masa kuma zai yaki abin.

Kamar yadda muka samu rahoto, an kawo takardun hukumar zaben ne a jakukkuna.

Idan har hakan ya faru, Dino zai zamo zababben dan majalisa na farko da aka yi wa kiranye.

Share.

game da Author