An kori manyan jami’an ‘yan sanda hudu

0

Hukumar Kula da Aikin ‘Yan Sanda ta amince da sallamar wasu manyan jami’an ‘yan sanda hudu. Wadanda aka sallama daga aiki sun hada da Mataimakin Kwamishina nan ‘yan sanda daya da kuma Mataimakan Sufurtanda uku. Duk an sallame su ne bisa dalilai na rashin da’a.

Babban jami’an hulda da jama’a na hukumar, Ikechukwu Ani, ya bayyana haka a Abuja ranar Laraba. Sai dai bai bayyana wa kamfanin dillancin labarai, NAN sunayen wadanda aka sallama din ba a cikin sanarwar da ya fitar.

Ya kuma kara da cewa an ladabtar da wani Mataimakin Sufurtanda daya, ta hanyar yi masa riktayar dole,
Har ila yau akwai wasu jami’an ‘yan sandan har 19 da aka labadtar inda wasu aka ba su takardar gargadi, wasu kuma aka ja kunnen su.

Share.

game da Author