Kwamishinan ‘yan sandan jihar Oyo ya gabatar wa manema labarai wasu da kae zargi da yin garkuwa da wani mutum, ciki kuwa har da dan sa.
Kwamishinan ‘yan sanda ya bayyana cewa sun cafke wani mutum da ake zargin cewa da hadin-bakin sa aka sace mahaifin sa.
Ya ce an sace mahaifin, an yi garkuwa da mahaifin mutumin ne a Karamar Hukumar Ibarapa ta Tsakiya tun a ranar 17 Ga Mayu, 2017 da karfe 6 na safe.
“Da mu ka tambayi wanda ake zargin, ya tabbatar da cewa an ba shi la’adar naira milyan daya daga cikin kudin diyya da aka biya aka saki mahaifin nasa.”
Jami’in ‘yan sanda ya ce wanda ake zargin ya ce mahaifin nasa bai yi masa laifin komai ba. Ya kara da cewa da zaran sun kammala bincike, za su tasa keyar wadanda suka aikata garkuwar zuwa kotu.