Amfani 5 da ‘ya’yan goji ke da shi a jikin Dan Adam

0

Banda samun iri na da za a shuka daga cikinsa ‘ya’yan goji na da matukar amfanin a jikin Dan Adam duk da cewa mafi yawan mutane ba su da masaniya akai.

Wasu masanna sun ce rashin sani ne ya ke sa mutane suke zubar da ‘ya’yan gojin kuma sun bayyana kadan daga cikin amfaninsa kamar haka;

1. ‘Ya’yan goji na dauke da sinadarin da ake kira Magnesium wanda ke da matukar amfani a jikin mutum.

Matsalolin da rashin wannan sinadari na Magnesium ke kawo wa a jikin mutum ya hada da cutar koda, cutar hawan jini,rashin karfin kashi, rashin karfin hakora, ciwon ido wanda ake kira ‘glaucoma’.

2. ‘Ya’yan goji na kawar da matsalar rashin haihuwa a jikin namiji domin yana dauke da sinadarorin vitamin B,C da D wanda suke taimaka wa namiji wajen haka.

3. ‘Ya’yan goji na dauke da sinadarin Tryptophan wanda ke hana mutum yawan yin fushi.

4. Yana kuma dauke da sinadarin Cucurbitacins wanda ke kare mutun daga kamuwa da cutar daji kowace iri.

5. Sinadarin Tryptophan na kuma taimakawa wajen samun barci musamman mutanen da ke samun matsalar rashinta.

Share.

game da Author