Sanin kowa ne a duk fadin karamar hukumar Gwoza garin Pulka ita ce mai dauke da ‘yan gudun hijira sama da dubu talatin wanda suke samun mafaka a garin.
A makon da ya gabata kungiyar bada agaji na likitoci mara iyaka (Doctors without boarder) wanda take gudanar da ayyukanta a garin tayi kira ga sauran hukumomi da su kawo dauki ga wannan gari dangane karancin ruwa da take fuskanta a lokacin da take karbar ‘yan gudun hijira sama da dubu uku wanda suka ketare daga Kamaru bayan share sama da shekaru biyu suna gudun hijira a kasar.
Al’ummar garin sun sha korafi amma sakamakon rashin layin sadarwa a yankin ba a jin muryarsu. Haka zalika ba a iya zuwa garin sai da rakiyar soja saboda fargaba.
Da Wannaan nake kira ga gwamnati da cewa ya kamata ta sani al’umar wannan gari na cikin matsanancin hali, kuma hakki ya rataya a wuyanta na magance wannan matsala.