Alkali ya dage Shari’ar Shema zuwa wata bakwai

0

Mai Shari’a Ibrahim Bako na Babbar Kotun Katsina, ya dage ci gaba da sauraron shari’ar da aka gurfanar da tsohon gwamna Ibrahim Shema, zuwa ranar 14 Ga Nuwamba, 2017. An gurfanar da Shema ne bisa zargin sa da ake yi kan wasurar kudade ko salwantar kudade naira bilyan 10.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai, NAN ya ruwaito, gwamnatin Katsina da hukumar EFCC ce suka maka Shema kotu, inda shi kuma ya garzaya Kotun Daukaka Kara a Kaduna, inda ya kalubalanci halascin kotun Katsina kan shari’ar sa da ta ke yi. An yi zaman ranar Talatar da ta gabata ne domin bangirorin biyu su bayar da bayanan da suka gudana a kotun Daukaka Kara ta Kaduna.

Mai Shari’a Bako, ya ce bayan ya saurari lauyoyin bangarorin biyu, ya fahimci ba shi da wani zabi sai fa ya daga tasa shari’ar.

“Na dage wannan shari’a zuwa ranar 14 Nuwamba, 2017.”

Lauyan EFCC, Ahmed El-marzuk, wanda kuma shi ne Atoni Janar na Jihar Katsina, ya fada wa kotun tun farko cewa Kotun Daukaka Kara ta Kaduna za ta yi bayani dangane da karar da Shema ya kai, a ranar 9 Ga Nuwamba.

Shi dai Shema an kai shi kara ne tare da Hamisu Makana, Babban Sakatare na Ma’aikatar Kananan Hukumomi, Lawal Safana, tsohon Shugaban Kungiyar Kananan Hukumomi, watau Lawal Dankaba.

Share.

game da Author