Tsakanin gwamnonin Arewa, Sarakuna, Matasan Arewa, Farfesa Ango Abdullahi da ‘Yan Kabilar Igbo

0

Idan akayi la’akari da yadda abubuwa suka yi ta faruwa a kasa Najeriya musamman a dan kwanakinnan za a iya cewa har yanzu akwai saurar rina a kaba musamman ganin yadda nan da watanni 12 za a iya cewa za a fara buga gangar siyasa.

Idan muka duba yadda siyasar ta jagule a musamman Arewa zaka iya cewa wannan karon ko Buhari ba zai yi wa wani dan takara tasiri ba.

Wani abu da ya ta da wa mutanen Arewa hankali a wannan makon da ya gabata shine yadda wasu sarakuna da gwamnonin Arewa suka yi ta maida wa kungiyoyin matasa da suka nemi ‘yan kabilar Igbo da ke yankinsu su tattara su koma garuruwan su nan da watanni uku masu zuwa.

Wadannan kungiyoyi na fitar da wannan sako sai gwamnan Kaduna Nasiru El-Rufai yayi maida musu da raddi sannan ya yi kira ga jami’an Tsaro da su nemo su duk inda suke su kamo su. Sannan ya umurci ma’aikatar shari’ar jihar ta shirya alkalai domin gurfanar da wadannan matasa a gaban kuliya.

Hakan bai tsaya ga gwamnan ba kawai, kungiyar gwamnonin Arewa suma suma su kayi Allah wadaran wannan kira na matasan Arewa sannan suka bukaci jami’an tsaro su hukunta matasan.

Sarkin Katsina, Mai martaba Abudulmumina Usman shi kuma a nasa nuna goyon bayan ga ‘yan Kabilar Igbo din cewa yayi wai zai iya sadaukar da jininsa domin kare su a jihar Katsina.

Duk wadannan kokari da shugabannin Arewa suka yi na ganin cewa sun nuna wa ‘yan kabilar Igbo din soyayya da zabin su gaba da nasu bai dada kungiyoyin su ‘yan kabilar Igbo din da kasa ba domin a wata martini da kungiyar MASSOB suka fitar bayan haka sun kalubalanci ‘yan Arewan da su kore su a yankin idan sun isa. Bayan haka ma sun ce shirin dama can na shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne da jam’iyyarsa APC.

Gwamnonin yankin Kudu maso gabas suma a zantawa da suka yi da manema labarai a gari Aba sun fito karara domin mara wa ‘yan kabilarsu baya da nuna fushinsu akan kiran da matasan Arewa din suka yi wa ‘yan kabilarsu mazauna yankin Arewan.

Shiko Farfesa Ango Abdullahi, shugaban kungiyar Dattawan Arewa cewa ya yi abin da matasan fadi ya yi daidai kuma yana tare dasu 100 bisa 100.

Ango Abdullahi yace dama can ‘yan kabilar Igbo basu dau dan Arewa da mutunci ba duk da sun watsu a yankin Arewar kamar kiyashi. Yace a kullum ci wa dan Arewa fuska suke yi.

Saboda haka bai ga dalilin da za a ce wai matasan Arewa sun fito sun nuna kishin yankinsu kuma gwamnoni su ce ba haka ba.

Mafi yawa da ga cikin wadanda suka tofa albarkacin bakinsu a akan wannan cecekuce tsakanin matasan Arewa, gwamnonin Arewa da na ‘yan kabilar Ibgo sun yi tir da halayyar shugabannin da gwamnonin Arewa.

Da yawa sun ba da misalin cewa babu irin rashin mutunci da cin fuska da ‘yan kabilar Igbo ba suyi wa ‘yan Arewa amma babu wani gwamna nasu da taba fitowa ya nuna abinda suke yi ba daidai bane sai dai ma su nuna suna tare da nasu.

“Ababen da suke amfana dasu a Arewa babu wani dan Arewa da yake iya samun wannan gatan a Kudu ba. Har kwanaki uku suka bada domin Biafra a kasa Najeriya amma babu wanda yace musu uffan sai namu. Gwamnonin mu sunyi shiru, nasu ma sun yi shiru amma daga cewa ga yadda muma ga matsayarmu kowa yayi mana ca.

Sun nuna goyon bayansu ga Ango Abdullahi da ya nuna gaskiya gaskiyace sannan ya tsaya akai.

Da yawa sun yabeshi da yi masa kirari da ‘Dattijo mai kishin Arewa’ sannan kuma daya da ya rage wa matasan Arewa.

Duk da cewa an bada umarnin a kama wadanna matasa da suka fitar da wannan zance har yanzu dai bamu ji komai akai ba.

Share.

game da Author