A kafa dokar hana ‘ya’yan jami’an gwamnati fita karatu kasashen waje – Sarauniyar Kyau

0

Zababbiyar sarauniyar kyau Chioma Obiadi ta yi kira ga gwamnatin da ta hana manyan ma’aikatan gwamnati tura ‘ya’yan su zuwa karatu kasashen waje.

Chioma Obiadi ne ke rike da kambun sarauniyar kyau na Najeriya.

Ta fadi haka ne da take tattaunawa da kamfanin dillancin labaran Najeriya inda ta yi kira ga gwamanti ta kafa dokar da zai hana ma’aikatan gwamnati tura ‘ya’yansu kasashen waje yin karatu.

Chioma ta ce irin haka ya sa ana ci gaba da nuna halin ko in kula wajen raya makarantun kasar nan saboda ‘ya’yansu basa karatu a ciki sannan barin haka zai sa a yi burus wajen kirkiro manufofi da za su taimaka wajen gyara harkar ilimin kasar.

Ta kuma bada misalin yadda jami’ar da take karatu a ciki wato jami’ar Nnamdi Azikuwe ke fama da matsalolin da ya hada da rashin ingantattun malamai da kuma kayayyakin koyarwa musamman na zamani.

Share.

game da Author