Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo yace Sakataren gwamnatin tarayya David Babachir da Ayo Oke na Hukumar Leken Asiri na ‘NIA’ suna nan a matsayin da suke na dakatar da su da akayi.
Mataimakin shugaban Kasar ya ce kwamitin da aka nada domin bincikan abin da ake tuhumarsu akai zai mika sakamakon bincikensa a daidai lokacin da ya kamata kuma ‘yan Najeriya za su san ko menene suka gano.
Tun kafin shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi tafiya ne ya nada Osinbajo shugaban wata kwamiti ta musamman domin ta binciki wadannan manyan jami’an gwamnati.
“Idan lokacin da ya kamata a fitar da bayanai akan sakamakon binciken yayi za a sanar wa ‘yan Najeriya komai dalla-dalla.” Inji Osinbajo.
Discussion about this post