Bayan tashin hankali da akayi a unguwan Kabala West jami’an tsaro sun shawo kan al’amarin inda komai yanzu yakoma yadda yake a da.
Kamar yadda rahotanni ya iske mu wasu matasa ne suka tada hankalin jama’ar yankin wai domin ganin gawa a makabartar Kiristoci dake yankin. Dalilin haka sai suka far ma wasu musulmai.
Hakan bai yi ma matasan musulmai dadi ba sai suma suka far ma kiristocin unguwan.
Ko da yake duk wadannan bayanai daga bakin mazauna unguwar ne muka samo, rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna bata bada bayanai akan ainihin abin da ya faru ba.
Jiragen saman yaki da jami’an soji da ‘yan sanda ne suka kai dauki unguwan tun kafin abin ya wuce gona da iri.
Kakakin gwamnana jihar Kaduna Samuel Aruwan ya sanar da cewa komai ya ya lafa domin gwamnati ta kai dauki cikin gaggawa.