Zabukan 2019 za su fi na 2015 inganci -Inji Shugaban INEC

0

Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa hukumar sa na bakin kokarin ta wajen tabbatar da cewa zabukan da za a gudanar nan gaba sun fi wanda aka gudanar a 2015 inganci.

Yakubu ya yi wannan jawabi ne yayin da ya ke karbar bakuncin Jakadan Amurka a Nijeriya, Stuart Symington a ofishin hukumar zabe, a Abuja. Ya kuma nuna godiyar sa ganin cewa Amurka ta nuna gamsuwar ta dangane yadda Nijeriya ta gudanar da zaben 2015.

A ta bakin sa, “Kun lura da cewa zaben 2015 ya tsaru sosai kuma an shirya shi a natse a cikin inganci. Sannan kuma ya yi daidai da dukkan ka’idojin zabe na kasa da kasa da aka amince da shi a duk diniya, sabanin zabukan can baya wadanda jama’a kan fito suna tayar da tarzoma kan tituna bayan gudanar da zaben.”

“Bayan kammala zaben 2015, an yi ta murna da kade-kade a kan tituna, wanda hakan wata alama ce da ke tabbatar da sewa an cimma nasarar gudanar da zabe, kuma ana kan turbar cimma ingantacciyar dimokradiyyar da Nijeriya ke so ta cimma.”

Dalili kenan a yanzu muke ta kara himma da daukar karin sabbin matakan ganin cewa zabukan nan gaba na 2019 za su ma fi na 2015 inganci.” Inji Yakubu, wanda ya kara da cewa yin kyakkyawan shirye-shirye na daya daga cikin hanyoyin kara inganta zaben 2019 mai zuwa.

Shugaban na Hukumar Zabe ya kara da cewa hukumar sa za ta ci gaba da tantancewa da aikin bada rajistar zabe a dukkan fadin kananan hukumomi 774 na kasar nan kafin 2019.

“A halin yanzu, ina mai sanar da kai cewa mu na da mutane masu rajista a kasar nan har milyan 70, kuma Amurka kadai ce kasa mai bin tafarkin shugaban kasa mai cikakken iko, wacce ta fi Nijeriya yawan masu kada kuri’u a duniya.”

Tun da farko, a nasa jawabin, Symington ya bayyana cewa wannan ziyara da ya kai wa Hukumar Zabe, ya je ne domin sanin yadda Nijeriya ta gudanar da zaben ta. Ya kuma yaba wa hukumar a kan nasarar zaben 2015.

Jakadan ya kuma ce kusan ra’ayoyin jama’a a duniya ya fi karkata wajen jaddada cewa zaben 2015 da Nijeriya ta gudanar, ingantacce ne, kuma sahihi da aka gudanar a cikin yanayi na zaman lafiya.

Share.

game da Author