Ya zuwa yanzu dai kwamitin mutane uku da Shugaban Kasa ya kafa karkashin shugabancin Mataimakin sa Osinbajo, ya kammala aikin binciken da aka dora masa na gano masu hannu kan satar makudan kudaden da EFCC ta kama a unguwar Ikoyi, Lagos da kuma na argin harkallar kwangilar datse ciyawa da ake zargen sakataren gwamnatin tarayya, Mista Babachir Lawal.
Rahotanni sun ce an dage ranar da za a gabatar wa Shugaba Buhari sakamakon zuwa ranar Litinin mai zuwa. Darakta Janar na hukumar tsaro ta NIA ne ake zargin ya damfare makudan kudaden da EFCC ta bankado a Legas, kuma tuni aka dakatar da shi, tare da Lawan.
Sauran ‘yan kwamitin sun hada da Ministan Shari’a Abubakar Malami da kuma Mai Ba Shugaban Kasa Shawara a fannin tsaro, Babagana Munguno. Tun da farko dai sati biyu Buhari ya ba su domin su kammala binciken, kuma yau ne wa’adin kammalawar ya kare.
Kakakin yada labarai na Mataimakin Shugaban Kasa, Laolu Akande, ya bayyana cewa an dage ranar gabatar da binciken daga yau Laraba, zuwa ranar 8 Ga Mayu, wato Litinin mai zuwa.
Yanzu dai hankulan ‘yan Najeriya ya karkata a kan jin sakamakon binciken wadannan manyan jami’an gwamnati da suka goga wa yinkurin gwamnatin na yaki da cin hanci da rashawa bakin fenti.