Kungiyar Clitoraid dake kasar Amurka ta sanar da shirin fara yi wa matan da aka yi wa kaciya aiki a gabansu domin samar musu da jin dadin da basa samu a lokacin da suke saduwa da namiji.
Za a fara aikin ne daga 2 zuwa 13 gawatan Mayu a Nairobi Kenya.
Mai magana da yawun kungiyar Nadine Gary ta sanar da hakanne a wani taron da kungiyar ta shirya domin fadakar da mutane kan illolin dake tattare da yi wa mata kaciya.
Nadine Gary ta ce an kafa kungiyar Clitoraid a shekarar 2004 kuma likitocin su su ka yi fida wa mata sama da 250 a kasar Amurka.
Daya daga cikin matan da kungiyar ta yi wa aiki a gabanta, Jaha Dukereh ‘yar kasar Gambia ta ce rayuwarta ya canza tun bayan aikin da akayi mata domin tana jin dadin rayuwarta fiye da da.