Za a samar da sabon shiri don horas da ma’aikatan Ungozoma a Najeriya

0

Gwamnatin Najeriya zata samar da sabon shiri na horas da ma’aikatan ungozoma domin inganta ayyukansu a asibitocin kasa Najeriya.

Ministan kiwon lafiya Isaac Adewale ne ya sanar da haka a taron ma’aikatan unguwan zoma na kasa da kasa na shekaran 2017 da aka yi a Abuja.

Ya kuma kara da cewa samun kwararrun ma’aikatan unguwan zoma na daya daga cikin hayoyin da zai taimaka wa musamman fannin kiwon lafiya da ya hada da ayyukansu a asibitoci kamar su karban haihuwa, wayar da kan mutane kan cin abincin da ya kamata suci, mahimancin amfani da tsaftacen ruwa da kuma tsaftace muhalli da sauran su.

“ Idan har aka gyara sannan aka bunkasa ayyukan unguwan zoma a asibitocin mu lallai za a samu dinbin nasara a harkar kula da marasa lafiya a asibitocin kasar nan.

Ya ce kamata ya yi gwamnati ta kafa hukumar kula da ci gaban ma’aikatun kula da kiwon lafiya na matakin farko a jihohin kasar nan wato State Primary Healthcare Development Agency (SPHCDA) domin taimakawa wajen samar da yanayin aiki mai kyau ga musamman ma’aikatan unguwan zoma.

Shugaban gidauniyar ‘’well Being’’ Sanata Toyin Saraki a nata tsokacin da tayi a wajen taron tayi kira ga kafanoni masu zaman kasu da su taimaka wajen bada tallafi ga asibitocin kasa Najeriya.

Share.

game da Author