Kungiyar ‘Alma Sana’ tare da hadin guiwar kamfanin sarrafa magunguna na Glaxosmithkline sun fitar da wata dabarar sakawa yara kanana wani abin da ake daurawa a hannu na roba wanda zai taimaka wajen tunatar da iyayensu lokuttan yi musu allurar rigakafi domin kare su daga cututtukan zamani.
Kamfanin Glaxosmithkline ne ta sanar da hakan a taron wayar da kai da aka yi ranar Alhamis a Abuja.
Shugaban kamfanin na rashen Abuja, Bhushan Akshikar ya bayyana cewa abin hannun da za a saka wa yaro zai taimakawa ma’aikatan asibiti da kuma uwayen yaran sanin lokacin da ya kamata a yi wa yaro allura da kuma irin allurar da ya kamata ayi wa yaro sannan kuma zai taimaka wa kasa Najeriya wajen kawar da matsalolin rashin yi wa yara allurar rigakafi.
Ya ce ma’aiaktan asibiti za su saka wa yaro wannan abin hannun da zaran an haife shi/ta a kafa sannan kuma a mai da shi a hannun yaron yayin da yake girma har na tsawon lokacin da dan zai bukaci alluran rigakafin.
Shugaban gidauniyar ‘Wellbeing Foundation Africa’ Toyin Saraki ta ce wannan dabaran zai taimaka wajen yi wa kowani yaro a kasarnan allurar rigakafi wanda hakan ke neman ya zama babbar matsala a kasa Najeriya.
Toyin Saraki ta kuma shawarci ma’aikatan asibiti musamman unguwar zoma da su ci gaba da wayar da kan mata mahimmancin yi wa yaran su alluran rigakafi.
Shola Dele-Olowu na kungiyar ‘Alma Sana’ ta ce za su yi aiki da hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko na kasa wajen gwada irin sakamakon da amfanin da abin hannun zai haifar wanda za su rabawa mutane ne kyauta sannan kuma zai taimaka wa mai’akatan asibiti wajen ba uwaye shawarar da ya kamata kan yin rigakafi ga ‘ya’yansu.